YAN'UWAN TAKA DA SHARUDDANTA
Allah madaukain sarki yana gaya mana acikin alqur,ani mai girma cewa 'innamal mu,uminina ikhwah' lalle muminai yan uwan juna ne dan haka yan uwantaka tare da kyakkyawan mu,amala ta wajaba ga musulmi dan mu,amala da kyawawan halaye suna daya daga abubuwan da yasanya da yawa suka shiga musulunci manzon Allah (s.a.w) ya koyar damu kyawawan halayensa dan mubi kuma Alla ya yabe shi cewa (Innaka la,ala khulqin azeem) lallai manzon Allah yana kan kyawawan dabi,u masu girma.
Manzon yayi haquri da mutane tare da mayar musu kykkyawa in har an masa mummuna to yana ramawa da kykkyawa babban misali abinda ya faru tsakaninsa da bayahude maqwabcinsa da yake sanya masa shara kullum aqofar gida amma bai taba masa magana ba, sai wata ran manzo ya fito gida bai ga shara ba ya tambaya ina mai zuba masa shara kullum aqofar akace ai bashi da lafiya sai fiyayyan halitta ya tafi ya duba shi bayan yaje yasameshi akan shinfidar mutuwa sai manzon Allah ya umarce shi da yayi kalmar shahada dan shiga musulunci sai ya karkata kai ya kalli babansa ,sai baban ya masa umarini da ya amsa kiran manzon Allah ,ya amsa yayi kalmar shahada ya musulunta kuma ya cika da imani.
kenan kyawawan halaye suna da kyau da jan yan uwamu a tafarki na gari.
Manzon Allah yana cewa (DAYANKU IMANINSA BAYA CIKA HAR SAI YASOWA KANSA ABINDA YASOWA DAN UWANSA)
SHARUDDAN YAN UWANTAKA;
- Takasance domin Allah.
- Takasance a musulunci.
- Takasance an yita tare da imani da tsoron Allah.
- Takasance angina ta dan yiwa juna nasiha domin Allah.
HANYOYIN BUNQASA YAN'UWANTAKA:
- Idan mutum yaji yana son dan uwansa ya sanar dashi.
- Idan ya rabu da dan uwansa to yaringa masa addu,a abayan idonsa.
- Idan ya hadu da dan uwansa yayi gaggawar masa sallama tare da musafaha(miqa masa hannu).
- Ya yawaita ziyarar dan uwansa lokaci-lokaci.
- Taya shi murna aduk lokacin da abin farin ciki ya sameshi da yi masa jaje idan wani abin baqin ciki ya sameshi.
- yi masa nasiha da wasiyya da haquri yayin rashi,ko masifa atare dashi, da yi masa ta,aziyya in an masa mutuwa.
- Ya tai maka masa aduk lokacin da buqatar hakan ta taso.
Allah yasa mu dace yasanmu daga cikin masu tsira.
wassalamu alaikum
