MARABA DA RAMADAN (2)
Yan,uwa .... Assalamu alaikum
Barkanku da sake haduwarmu a maraba da ramadan kashi na (2).
Ya inganta manzo (s.a.w) yana yiwa sahabbansa bushara da zuwan watan azumi, manzon Allah yace"Idan farkon daren azumi ya kasance ana bude qofofin aljanna gaba daya ba tare da an rufe ko qofa daya ba, kuma ana rufe qofofin wuta baki daya ba tare da an bude ko guda daya ba, kuma akatange shaidanu,sai mai kira yayi kira ina mai neman alheri ya kusanto, ina mai neman sharri ya qaranta, Allah yana da yan'tattu daga wuta akowane dare."
Azumi na da falalar gaske daga ciki akwai shu,urin cewa dukkan al,umma dayane suna cin abinci lokaci daya kuma suna kame baki alokaci daya, mai kudi zaiji ni,imar wadata sai ya taimaka ma talaka,kuma yana qara tsoron Allah.
ABUBUWAN DA SUKA KAMACI MAI AZUMI;
- Yawaita biyayya ga Allah tare da gujewa abubuwan da aka haneshi yayi da kiyaye farillai, da nisantar abubuwan da aka haramta.
- yin sallah akan lokaci da halartar jam,i ga namiji cikin sallolinsa biyar dan manzon Allah yayi umarni da yin sallah acikin jama,a har yake cewa naso ace na umarci wani yaja sallah ni kuma in bi wadanda basa halartar sallah da jama,a da qirare na wuta aqona su, dan haka zamuga sallah a jam,a akwai shi da muhimmanci tunda har manzon Allah ya fadi hakan.
- Nisantar qarya da cin naman mutane (gulma) da algus da mu,amala da riba ga yan'kasuwa da duk wani aiki ko magana wanda yake haram ne.Manzon Allah yace" wanda bai bar fadin qarya da aiki da ita ba da jahilci, Allah baya buqatarsa da yabar ci da sha dan shi."
- Nisantar almubazzaranci a wajen abinci fadin Allah madaukakin sarki( kuci kuma ku sha amma kada kuyi israfi(barna) dan Allah baya son masu israfi) in yayi yawa to abayar sadaka.
- Yin sallar tarawih (asham) a maallaci tare da jama,a tare da tsoron Allah da kuma halarto zuciya ayayin yin sallah , yawaita nafilfilin dare da na rana.
- Yawan karatun alqur,ani da neman sanin fassararsa, da yawaita addu,o,i, sadaka, agazawa mai rauni, ciyar da mai azumi abin buda baki, yazo ahadisin manzon Allah (s.a.w) "wanda ya ciyar da mai azumi abin buda baki yana da kwatankwacin ladan mai azumin ba tare da an rage ladan mai azumin ko kadan ba. kuma an gafarta masa zunubansa an yan"tashi daga wuta" Allah yana bada ladan ga wanda ya baiwa mai azumin abinda zai buda baki ko da madara,ruwan sha, dabino. duk wanda ya shayar da mai azumi Allah zai shayar dashi daga qoramar manzon Allah.
- umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, kiyaye kai daga abubuwan da basu da amfani.
- Fidda zakka ga mutumin data wajaba akansa in har lokacin fitarwa yayi kafin azumi ko bayan azumi,amma in yasaba ma kansa fidda zakka din a azumi yana da kyau saboda samun miskinai da masu rauni da kuma ninkuwar ladan ayyuka a wannan wata mai alfarma.
Yan"uwana musulmi Allah yasa mu dace ya kuma sanya muna cikin yan tattu daga wuta.
ameen
wassalamu alaikum warahmatullahi ta,ala wabarakatuhu.
No comments:
Post a Comment