MARABA DA MAI ALBARKA
Godiya ta tabbata ga ubangijin da ya sanya ramadan watane na kankare zunubai da qara lada da daga darajojin dan adam , ramadan watane farkonsa rahma,tsakiyarsa gafara ,qarshensa yan' tarwa daga wuta.
abubuwan da yakamata mai azumi ya gudanar dasu yayin zuwa wannan wata mai albarka ;
1) TSORON ALLAH ; duk lokacin da ka kiyaye biyayya ga allah kuma zuciyarka ta cika da tsoron allah tare da ganin girmansa da tsoronsa, domin shi tsoronsa shine zuciyarka taji tana binsa kuma tana hanuwa da dukkan abinda ya hana.
tsoron allah yakansa mutum yayi abu tsakaninsa da mahaliccinsa kamar yadda yazo acikin tarihin zainul abidyn (ya kasance tsawon shekara 10 yana ciyar da mutane babu wanda ya sani har sai da ya mutu anzo masa wanka aka ga abayansa akwai alamar dan dako gashi, shi ba dan dako ba sai akaji kuma gidajen talakawa a madina suna kukan basu da abinci alhali sun kasance in suna tashi da asuba suna karo da buhun abinci aqofar gida ba tare da sun san wa ya aje ba sai da zainul abdyn ya mutu suka ga abinci ya dauke suka san wa ka aje musu, yayi hakane dan ya kasance aikinsa tsakaninsa da allah ne kawai ba tare da wani dan adam ya sani ba). dan haka ake son mutum ya kasance yana da aiki da yake ba wanda ya sani daga shi sai mahaliccinsa kamar yadda sahabbai da dama sunyi hakan hasanul basari yake cewa ( mun riski wasu daga sahabbai dayansu yakan kasance tare da iyalinsa ashinfida amma idonsa na zubar da hawaye na tsoron allah ba tare da iyalinsa sun san me ke faruwa ba) kuma sukan hadu daya ya zubda hawayensa don tsoron allah amma yana boyewa kar dan uwansa ya san me yakeyi allah yasa mu dace.
2) ADDU,A; koda yaushe dan neman tsoron allah ( allahumma inni a,uzu bika an ushrika bika shai,an a,alamuhu wa astagfiruka lima la a,alam.
3) TUBA; ka tuba ga allah ga dukkan zunubanka tuba na gaskiya fadin allah madaukakin sarki;( ku tuba zuwa ga allah baki dayanku yaku muminai ko kwa samu babban rabo.)
yan uwan musulmai ina muku murna da isowar wannan wata mai alfarma tare da yasamu cikin yan tattu daga wuta.
yar,uwarku
amatullah hajir ( um_ ja,afar)
No comments:
Post a Comment