Tuesday, December 16, 2008

UWARGIDAN MAJI DADI (3)

..... shugabanmu Annabi Ibrahim (A.S) itace uwar Annabi Ishaq (A,S) kakar Annabi ya,aqub (A,S) Uwar kakar Annabi yusuf (A.S) maqociyarmahaifiyar Annabi Isma,el (A.S) (hajir).
Gareta duk dangantakar Annabawan bani isra,ela ta bangaren uwa ta qare tun daga kan Annabi musa, haroun, Dawud,Sulaiman,Zakariyya,Yahya,Uzair,Armaya,u, Isa (A.S) dasauransu.

SARAH TA AURI MAJI DADI
Annabi Ibrahim maji dadin Allah ya auri sarah yar" baffansa kuma ya sota so mai tsanani saboda addininta dakuma dangantakarta dashi takasance mai gaskiyar imani.


sarah ta shiga yanayin rayuwa guda biyu:-
1) yanayin jarabawa.
2) yanayin daukaka da amsa addu,a.
YANAYIN JARABAWA:-
Alokacin da sarah da Annabi Ibrahim sukayi hijra zuwa garin misra, awannan lokacin sarkin misra shine amru bn imru,ulqais bn mayaalun kafirine kuma fajiri mai zalunci, wanda alokacin shine sarkin sarakunan da ya gagaresu, in har yaso mace kyakkyawa a wannan lokacin oda tana da aure sai dai mijinta yasakar masa ita inkuma yar' uwarsa ce sai ya qyaleta.
Ansamo hadisi ingantacce fadin manzon Allah (s.a.w) cewa(Annabi Ibrahim bai qaryaba sai awuri uku.......)
mu hadu a uwargidan maji dadi kashi na hudu(4)

No comments: