UWARGIDAN MAJI DADI (2)
Ita dai wannan baiwar Allah mai laqabi da "Uwargidan maji dadi" wacce take cikin matan da ya kamata ayi koyi dasu itace: Matar annabi kuma manzo, mahaifiyar annabi,kakar annabi,mahaifiyar kakar annabi,maqociyar mahaifiyar annabi, tana da dangantaka da annabawa da dama.)
"An karbo daga yusif dan abi ishaq daga babansa yace" fatima yar manzon Allah tace da mahaifinta ya manzon Allah rayuwata bazata amfaneni ba har sai ka tambayi Jibril dangane da mahaifiyata, sai ya tambayehi ya amsa masa da cewa " tana tsakanin Maryam da Sarah a aljanna"
Nasan mai karatu ta fara jiyo qamshin wacece Uwar gidan maji dadi???????
Uwargidan maji dadi yar aljannace takasance abisa rabi kyawun hauwa,u uwar al,ummah, itace matar annabi,manzon Allah daya daga ciin manya-manyan mazanni, nabiyun fiyayyen halitta, baban annabawa, maji dadin Allah shugabanmu...........
mu hadu a "Uwargidan maji dadi kashi na uku (3)
amatullah khamis haroun (umja,afar)
No comments:
Post a Comment