Friday, May 4, 2007

TA,AZIYYAR JA,AFAR MAHMUD ADAM

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

TA,AZIYYAH

إنا لله وإنا إليه راجعون

TA,AZIYYAR SHAHIDI JA,AFAR MAHMUD ADAM

YA SHAHIDIN AL,UMMAH

Shakhsiyyar da Nigeria bazata manta ta ba atarihi, saboda abinda ka gabatar a fagen kira ga Allah; ka karantar da mutane, ka tarbiyantar da matasa, ja,far na amince da kai, amintaka ta gasiya, gashi yau kabar wannan duniya mai qarewa, ka tafi gidan da ka dade kana jiransa, a gaskiya kayi shahadar da kowa yasan shahada ce, ja,afar yau ka kai matsayin da kake burin ka kai, ka bar mutane a cikin rudu saboda kasancewar ka al,ummah, matsayin shahada shine burinka, kuma dama duk wanda yayi burinta allah zai bashi ita koda akan gadonsa ya rasu!!! .
TO ! ja,afar ga tarihi yana mai-maita kansa, ka bar duniya abisa tafarkin daya bar na ukun mafiya alherin wannan al,ummah da matsayi wato amirul mu,uminina sayyidna umar bin khattab (R.A), ga ka yau ka bar duniya a hannun maqiyan al,ummah wanda basu san matsayin malamai ba, bare mutunta masallaci, da jinin musulmi dake da girma awajen Allah, Allah ya biya maka buqatarka ja,afar, muma in sha Allahu kan tafarkin ka zamu wuce, da hanyar da kabi,kuma manufarka muke riqe da ita, ja,afar matsayinka agun al,ummah kamar rai ne ajikin dan adam; ba Nigeria kawai da,awarka ta tsaya ba har ma da wasu qasashe, son da mutane ke maka yakance musu fitra, ka fitar da mutane daga jahilci, da bata izuwa hasken gaskiya da shiriya ( daga muminai akwai mazaje da suka cika alqawrinsu ga Allah sukayi haquri akan duk wani baqin ciki,cuta,daga cikinsu akwai wanda ya cika bakantarsa yayi shahada a tafarkin Allah ko ya mutu akan gasiya da alqawari,daga cikinsu akwai mai jiran dayan biyun:nasara, ko shahada basu canja alqawarin Allah ba kuma basu fasa cika alqawarin ba, kamar yadda munafikai suka canja) (surah: Ahzab,23 tafsir muyassar) kana daga ciKinsu ya ja,afar , Allah yan cewa :( dukkan mai rai mamaci ne) (surah: Ali-imran,185), Allah yayi gaskiya azancensa, matsayin shahada yana da girma! Allah yanA gayawa Annabinsa Muhammad (s.a.w) (kada ka zaci wadanda aka kashe akan tafarkin Allah matattune, a,a suna nan da ransu awajen uban gijinsu ,rayukansu na tashi acikin aljanna kamar yadda tsuntsu ke tashi suna cin ya'ya'n itatuwan aljanna kamar yadda yazo a hadisi. Suna masu farin ciki da abinda Allah ya basu na falalarsa,suna ma yan' uwansu na bayansu da basu iso ba bushara da cewa suna nan al,ajanna cikin aminci ba tsoro kuma ba baqin ciki)(surah:Ali-imran 169-170. tafsir jalalain)
na farkonsu shine sayyidna Hamza,zakin Allah, shugaban shahidai .
Wanda duk yayi wannan mumunan aiki yayi asarah!!!!!
uqubar Allah mai tsanani ce ga wanda ya saba umarninsa.
Ja,afar ya isheka alfahari an kashe ka kana sujjada ga ubangijinka wannan shine tafarkin salihai, an kashe ka azalumci,( duk wanda aka kashe a zalumce,mun sanya ma waliyyinsa ya dauki fansarsa ba tare da yayi israfi ba (wuce qa,ida awajen daukar fansa ) awajen kisa ,kuma lalle Allah mai taimakon waliyyin ne har ya dauki fansa) (surah:Al-israa,33.tafsir almuyassar)
Haqiqah ja,afar matsayinka ya bayyana yayinda yazama qarshen surar da ka karanta a alqur,ani a sallar asuba kuma a,ita za,a tasheka ranar alqiyama itace suratul ma,arij, wadda ke qunshe da abubuwa da dama, daga ciki akwai fadin Allha madaukakin sarki (kayi haquri,haquri mai kyau, suna ganin (azabar) da nisa,mu muna ganinta akusa) (surah:Al-ma,arij,5-7)
Sannan acikinta akwai (shi dan adam an halicceshi mai girgizane, idan wani abinda baya so ya same shi sai yaringa raki, amma idan alheri ya sameshi sai ya ringa kaffa-kaffa da shi yana riqewa ,sai dai masallata ( mumunai sune basa yin hakan) (surah: Al-ma,arij 18-22 tafsir jalalain) kuma acikinta ne Allah yake fadar suffofin mumuminai ( wadannan sune ake karramasu a,aljannah) surah:Al-ma,arij 35, haka yazo acikin hadisi ran lahira za,ace da makarantan al,qurni:( karanta kamar yadda kake karantashi aduniya ,matsayinka a qarshen ayar da ka tsaya awajen karatu) muna ma fatan ka kasance cikinsu ya ja,afar.
An kasha ka kana mai-maita kalmar shahada(LA,ILAHA ILLALLAH MUHAMMADUR RASULILLAH).
Manzon Allah yan cewa ( duk wanda qarshen maganarsa a duniya ta zama la,ilaha illallah zai shiga aljanna), an kashe ka ranar juma,a, hadisai sun inganta duk wanda ya mutu ranar juma,a ya kubuta daga azabar qabari da fitinarsa.
Dubban jama,a suna maka addu,a da nema ma rahama da gafara wajen ubangiji, tare da fatan Allah ya isar da matsayinka ,matsayin shahidai da salihai, ka bar mana alheri da dama ba adadi, kuma ladan zai bika har qiyamah.( idan bawa ya mutu ayyukansa sun yanke sai guda uku…) daga ciki akwai ilmi da ake amfanuwa da shi, sadaqace jariya.
Akwai mutanen da sun mutu amma kamar suna raye, akwai wadan suna raye amma matattu ne.
Ja,afar muna roqon Allah ya saka maka da alheri da abinda ka qaddamar wa al,ummah. Kuma ya tasheka ranar qiyama tare annabawa,masu gaskiya, shahidai, salhai, wadannan sune mafi kyawun abota acikin aljanna.


No comments: