Tuesday, May 8, 2007

SIFFOFIN DALIBAN QWARAI ( NA DAYA)

SIFFOFIN DALIBAI NA GARI (na daya)

Daga cikin siffofin dalbai na gari akwai yiwa juna wasiyya a duk in da suka hadu kamar yadda duk lokacin da sahabban manzon Allah suka hadu sai sun karanta suratul asr dan yiwa juna wasiyya.
Ku biyoni dan jin hirar qaruwa da ta kasance tsakanin saajidah da shahad a yayin da suka hadu suna ganawa tsakaninsu.



Saajidah: Assalamu alaikum wa rahamatullah
Shahad: wa alaikumu ssalamu wa rahmatullah
Saajidah: shahad ya hutu?
Shahad: hutu alhamdu lillah…. Ya naki hutun?
Saajidah: alhamdu lillah kwanaki yanzu gudu suke wai har hutu ya qare kamar yau ne mu kayi jarabawa muka yi hutun sati uku amma har ya qare.
Shahad: haka nima na gani ban je ko ina ba sai katsina dan yin sati wajen yayyen mahaifiyata.
Saajida: amma ina farin cikin dawowa makaranta dan qaruwa da muke kullum acikinta.
Shahad: hakane qwarai da gaske dan nima acikin hutu na halarci wasu karatuttuka na makarantun islamiyya masu amfani a katsina wanda ya qunshi hadisai dake kwadaitar da ayyuka na gari tare da bayanin sakamakonsu ranar lahira.
Saajida: dan Allah shahad qarad dani daga cikin abinda kika sani nima na qaru.
Shahad: kina son Allah ya yi miki salati?
Saajidah: qwarai da gaske ina fatan Allah yayi min salati dan nasamu rahmarsa.
Shahad: manzon Allah (S.A.W) yace:( Ba wani bawa da zai min salati face Allah yayi Masa salati goma a maimakon wannan dayan).
( ruwayar muslim)
Shahad: kina son gida al,ajannah?
Saajida: qwarai da gaske duk wani mumini yana fatan samun hakan.
Shahad: manzon Allah yace:(Babu wani bawa musulmi da zai sallah goma sha biyu nafila ba farillah ba a rana dan Allah ma daukakin sarki face allah ya gina masa gida a,aljannah. (ruwayar muslim)
Saajida: shahad gaskiya babu abinda yafi addinin Allah sauqi in banyi ba ba za,a rubuta min alhaki ba kuma inna yi za,a gina min gida al,ajannah, Allah yasa mu dace.
Shahad: shin kinji wannan wasiyyar?
Saajidah: wace wasiyyah ce?
Shahad: hadisi ne abu hurairah yake cewa:( maji dadi na manzon Allah (s.a.w) ya min wasiyyah da yin azumi uku cikin ko wane wata, da yin sallah walha raka,a biyu, sannan kar nayi barci har sai nayi wuturi).(ruwayar bukhari da muslim)
Saajida: dama sallar walha raka,a biyu ce?
Shahad: a,a tazo a wani hadisin zaki iya yin raka,a hudu ko raka,a
takwas.
Shahad: shin kina so ayyukank nagari su zarce bayan rasuwarki?
Saajida: sosai ma kuwa dan in mutum ya mutu kuma ba wani aiki da zai. iya yi.
Shahad: daga cikin ayyuka na gari dake zarcewa bayan rasuwar mutum sune: gina Masallaci,gina rijiyoyi, yada ilmi kamar buga littatafai dan yadasu da Kasusuwan fadakar wa dan sadaukar wa ko taimakawa da dukiyar da za,ayi Wadannan hidimomi. Manzon Allah yana cewa :(Idan mutum ya mutu duk Ayyukan sa sun yanke sai dai guda uku: sadaqa jaariya, ko ilmi da ake amfanuwa dashi, ko da na gari yana masa addu,a.(ruwayar muslim)
Saajida: shahad kin san burina shine in zama malamar makaranta in mun gama karatu ,Allah yayi mana jagora.
Shahad: ameen, nima ina fatan naga na rubuta littafai da dama dan wayar da kan al, Ummah.
Shahad: kina son Allah ya amsa addu,arki?
Saajida: me zan yi in samu hakan shahad?
Shahad: manzon Allah(s.a.w) yace :Ba wani bawa da zai yiwa dan uwansa addu,a ba tare Da shi dan uwan yasan yana masa addu,a ba face mala,ika yace kai ma kana da kamar abin da ka roqa qa dan, uwanka).(ruwayar muslim)
Saajida: kenan ya kamata mu ringa yiwa yan" uwanmu addu,a da duk wani musulmi a Kan doron qasa tare da fatan Allah ya daukaka musulunci.
Shahad: shin kin san wane zance ne Allah yafi so yaji daga bayinsa?
Saajida: wane zance ne? zanso naji.
Shahad: manzon Allah (s.a.w) yace:( bana baku labarin zance mafi soyuwa a wajen Allah ba? Lallai zance mafi soyuwa awajen Allah shine: SUBHANALLAHI WABI HAMDIHI) (ruwayar
Muslim).
Shahad: kina so Allah ya gafarta miki zunubanki ko da suna da yawa?
Saajida: na,am shahad inna tuna haduwata da uban giji nakan ji hankali
Na ya tashi saboda dan adam mai yawan kura-kurai ne wanda ya
Ya sani da wanda bai sani ba.
Shahad:albishirinki saajida manzon Allah (s.a.w) yace( wanda duk yace(
SUBHANALLAHI WABI HAMDIHI) a rana sau dari an kan
Kare masa zunubansa ko da kuwa sun kai kumfar kogi.(ruwayar
Bikhari da muslim)
Shahad: sannan kina so ki zama kin kusanci ubangiji.
Saajida: ba abinda yafi hakan dadi a wajen bawa ya kusanci ubangijinsa.
Shahad: manzon Allah (s.a.w) yace: "bawa yakan kasance mafi kusanci
Da ubangijinsa lokacin da yake sujjada, ku yawaita addu,a.(ruwayar bukhari da muslim)
Ga shi sunanki saajida yana nufin mai yawan sujjada.
Saajida: shahad ke kuma menene ma,anar sunanki?
Shahad: ma,anar sunana daga shahadane na kalmar shahada wato shaida.
Saajida: nagode qwarai da gaske, haqiqa na qaru sosai dan haka halartar bita, ko kwasa-kwasai yana qarawa mutum haske da ilmi arayu
Warsa dan zai san abubuwa da dama da bai sani bad an ilmi kogi
ne.
Shahad: bari in barki anan sai mun sake haduwa zan qarasa sauran daru
Ssan da na qaru dasu a hutu. Assalamu alaikum.
Saajida: wa alaikumussalam wa rahmatullah wa barakatuhu.


Anan hirar saajida da shahad ta qare sai karo na biyu domin jin abinda ya gudana tsakanin wadannan dalibai masu himmar karatu.


No comments: