Inna akramakum indallah atqakum
Haqiqa sau da dama mukan ga dan adam muyi masa hukunci da kamarsa da take a fili saboda ta saba ma matakan daukaka a idonmu, sau dayawa akan dauki matsayi abawa dan adam dan shi mai kudine ko mulki ko dan wata dan gantaka da yake da ita ko sanayya ta hanyar daukakar da danginsa keda shi agari … amma al,amarin ba anan yake ba akwai bayin Allah da ke yawo akan qasa wanda keda cikakkiyar dangantaka mai qarfi tsakaninsu da Allah saboda biyayyar da suke ma ubangijinsu, suna nan da ma mukan gansu a idonmu basu da qima amma ta yiwu ranar lahira mu riqa fatan samun matsayinsu saboda ni,ima da ubangijinsu ya musu kamar yadda yazo a hadisin manzon Allah(s.a.w) :
An karbo hadisin daga abu hurairah (R.A) yace:''manzon Allah (s.a.w) yace:''Ta yiwu mutumin da yake yayi futu-futu wanda aka turashi can bakin qofa da zai yi rantsuwa ga Allah da yabi masa rantsuwarsa ( ruwayar bukhari)
Dan haka ta yiwu naga mutum a qasqance amma ban san matsayinsa awajen ubangijinsa ba.
No comments:
Post a Comment